Haɗin kai tsakanin DW da Freedom Rediyo
September 19, 2008Talla
Cuɗanya tsakanin Gidan Rediyon Deutsche Welle da na Freedom dake Kano a tarayyar Nigeria na cigaba da ingantuwa musamman ta fannin aiki, inda wannan gidan rediyo dake Kanon Dabo ya ba da ɗakunan shirye shiryensa inda aka haɗa sabon shirin Ji Ka Ƙaru. Ko ta yaya kafar yaɗa labaran na Freedom mai zaman kansa ke ganin wannan dangantaka? Sai a saurari hirar da Rabi Abubakar Gwandu ta yi da Alhaji Umar Dutse Mohammed shugaban Freedom Rediyo dake Kano.