1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

280408 Dialog Netzwerke

Fariborz, Arian May 22, 2008
https://p.dw.com/p/E4Xd
Taswirar ƙasar IndonesiaHoto: APGraphics

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, wanda a ciki muke duba batutuwan da suka shafi  addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´ummomi daban daban a wannan duniya ta mu.


Mafi yawa na al´ummar ƙasar Indonesia musulmi ne masu sassaucin ra´ayi waɗanda ke maraba da sauran mabiya addinai daban daban. To sai dai a saboda ƙaruwar matsaloli na zamantakewa yanzu ana samun rikice-rikice na addini. Yanzu haka wata haɗaɗɗiyar ƙungiyoyin musulmi ta tashi haiƙan don magance wannan matsala.


Har halin da ake ciki ƙasar Indonesia na matsayin abar koyi na kyakkyawar zamantakewa da zaman lafiya tsakanin ƙabilu da ƙungiyoyin addinai daban daban. Haɗin kai a cikin abubuwa daban daban masu tarin yawa, wannan dai ita ce manufar da ƙasar ta Indonesia ta sa a gaba a ƙoƙarin samar da kyakkyawan yanayin zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka tsakanin addinai daban daban kamar musulunci, Buddha, Hindu da kuma yarurruka da al´adu na al´ummomin wannan ƙasa. To sai dai sakamakon ƙaruwar matsalolin rayuwa musamman a ƙarshen shekarun 1990 ya sa rikice rikice masu nasaba da addini da kaiwa tsiraru hari da ɓullar ɗaiɗaikun ƙungiyoyin addinai na barazana ga kyakykawar zaman lafiya tsakanin al´ummomin ƙasar.


B: Ƙarshen zamanin mulkin kama karya na Suharto a shekarar 1998 da farkon sauye sauyen da aka samu a Indonesia a ƙarshen shekarun 1990 sun samar da wani yananyi na demukuraɗiya da kuma walwala a faɗin ƙasar. To sai dai ba ba jam´iyu da ƙungiyoyi da al´ummomi masu son zaman lafiya da juriya da raɗin girke demuƙuraɗiya kaɗai suka ci gajiyar wannan sabon yanayi ba, a´a har da ma masu tsattsauran ra´ayin addinin musulunci.


A: A dai halin da ake ciki ana samun ƙaruwar ƙungiyoyin musulmi dake da manufa ta siyasa a ƙasar ta Indonesia. Ƙungiyoyi kamar Islamic Defensive Front ko jam´iyar adalci da wadata suna wa´azi ne bisa wata fassara ta masu ra´ayin riƙaun addinin musulunci. Suna kira da a kafa dokar shari´ar musulunci a duk faɗin ƙasar sannan suna yaƙi da duk wani abin da suke zargin cewa fasiƙanci ne ko haramun ne a cikin addini.

.......

Don tinkarar yaɗuwar tsatsauran ra´ayin addinin Islama a cikin wannan ƙasa mafi yawan musulmi a duniya baki ɗaya, yanzu an kafa ƙungiyoyin musulmi masu sassaucin ra´ayi. Daga cikin su kuwa akwai ƙungiyar haɗaɗɗiyar ƙungiyar musulmi masu sassaucin ra´ayi wato Liberal Islamic Network. Sugaban ƙungiyar Lutfi Assyaukanie burin da suka gaba na tuntuɓar juna tsakanin mabiya addinai daban daban.


B: "A cikin shekara ta 2001 aka kafa ƙungiyar a matsayin wata ƙungiya mai zaman kanta. Burin mu shi ne mu haɗa kan sauran ƙungiyoyin musulmi masu manufa ta sassauci tare da musayar ra´ayoyi a tsakani. Mun yi shirya tarukan ƙarawa juna sani, gudanar da shawarwari da jama´a da wasu shirye shirye a gidajen rediyo. Mun kan yi tattauna game da ƙalubalen da ke gaban al´ummar musulmi bayan murabus ɗin shugaba Suharto. Yanzu muna cikin mulkin demuƙuraɗiya saboda haka idan ba mu yayata manufarmu ba to wasu zasu cike wannan giɓi da wata fassara daban ta addinin musulunci. Muna matsayin wata amsa ga ƙaruwar tsattsauran ra´ayin Islama a Indonesia."


Ƙungiyar Liberal Islamic Network ta Lutfi Assyaukanie ta ƙunshi matasa da kuma masana kimiyar addinin musulunci. Sun dukufa wajen aikin tuntuɓar juna tsaƙanin addinai da ci-gaba da bin tsarin mulki da babu ruwansa da addini da ƙarfafa haɗin kan al´ummomi daban daban a ƙasar ta Indonesia. Ƙungiyar na adawa da fassara Al-Qur´ani mai girma ba tare da la´akari da sauyin zamani ba wato kamar ´yancin faɗin albarkacin baki, ´yancin mata da nuna juriya da wasu addinai ko rashin girmama tsiraru ba. Wata ƙungiyar da ita ma take bin wannan manufar ita ce wata ƙungiyar matan Indonesia da ake kira Rahima. Ƙungiyar wadda aka kafa ta shekaru takwas da suka wuce tana gwagwarmayar ganin an bawa mata ´yanci daidai da yadda addinin musulunci ya tanada da kuma ba su cikakken wakilci a fagen siyasar ƙasar. Babban aikinta shi ne tafiyar da wata makarantar Islamiya ta Intanet da kafa wasu cibiyoyin musulunci inda za a riƙa yaɗa sabuwar fahimtar addinin. Shugabarta Aditiana Dewi Erdani ta yi bayani tana mai cewa.      


O-Ton Aditiana


„A lokacin da muka kafa ƙungiyar Rahima  babban burinmu shi ne mu yi ƙoƙari aikin da muke yi na makarantar yanar gizo ta musulunci ya kai yankunan karkara. Mataki na biyu shi ne mu ƙara ilimantarwa da malaman waɗannan makarantun yadda zasu naƙalci sabuwar hanyar koyarwa. Yanzu haka dai muna horas da mutane a matsayin wakilanmu waɗanda kuma suke yaɗa manufar ta sassaucin ra´ayin addini musamman a tsakanin ɗalibai da kuma malamai. „


A ƙoƙarin su na yaɗa manufofi na sassaucin ra´ayi da yawa daga cikin ƙungiyoyi masu zaman kansu na bin hanya iri ɗaya. Alal misali ƙungiyar Rahima ta shafe shekaru tana haɗin guiwa da cibiyar Wahid wadda aka sa mata sunan tsohon shugaban Indonesia kuma shahararren malamin addinin musulunci a ƙasar Abdurrahman Wahid.

.....

Ita ma cibiyar ta Wahid dake zaman wata ƙungiya mai zaman kanta tana bin manufar girmama sauran addinai da aiwatar da sauyi irin na demuƙuraɗiya a Indonesia. Muƙadasshin daraktan cibiyar Ahmad Suaedy ya ce su ma suna mayar da hankali wajen inganta makarantun intanet na Islama.


O -Ton Ahmed Suaedy:


"Muna sauƙaƙawa mafi rinjayen musulmi waɗanda ba fitowa fili su yi magana, malamai na makarantun intanet na islama da shugabannin yankuna yadda zasu iya yaɗa manufofin musulunci da zaman lafiya, musulunci da zamantakewa. A wasu yanukan muna wayarwa da mutane kai yadda zasu fito fili su yi magana musamman ta gidajen rediyo da jaridu. 


Manufar dukkan ƙungiyoyin masu sassaucin ra´ayin musuluncin shine rage kaifin angizon masu tsattsauran ra´ayi ta hanyar ba da ilimi da tuntuɓar juna a matsayin mabuɗin fahimtar juna a ƙasar ta Indonesia mai al´ummomi daban daban.