1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haɗarin jirgin sama a Cameroun

May 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuLz

Masu aikun ceto a ƙasar Kamaru, da kyar da jiɓin goshi sungano gano tarkacen jirgin saman nan mallakar ƙasar Kenya, da yayi „salla da ka“, jiya a surmuƙuƙin kurmin Kamaru, tare da mutane 114 a cikin sa.

Jiya ne jirgin samparin Boeinga, ya tarwatse, a kan hanyar sa, ta zuwa Nairobi, babban birnin Kenya jim kaɗan bayan tashin sa daga Douala.

Matsaloli da su ka dabaibaye gano tarkacen wannan jirgi, cikin gaggawa, sun haɗa da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, da ake tabkawa a ƙasar ta Kamaru,da kuma sarƙƙaƙiyar itatuwa.

An gano wannan jirgi ɗazunnan a yankin Mvengue, da ke kudu maso yammacin Yaounde, to saida sanarwar ba ta bayana, yawan asara rayukan da aka yi cikin haɗarin ba.