Gwanayen sassake-sassake daga Yammacin Afirka
Kasar Cote d'Ivoire na da gwanayen masu fasahar sassaka. Sai dai ba su shahara ba kasancewa suna aiki ne ba da sanin kowa ba. Wani bikin baje koli da ake yi a zauren fasaha na tarayya da ke Bonn ya fito da aikinsu fili.
Cimma buri
A karni na 19 da 20 wasu kabilu daban-daban shida sun sassaka dodannin fuska a kasar Cote d'Ivoire da ke Yammacin Afirka. Shekaru gommai ba a ba wa aikinsu daraja ta gwanayen fasaha ba. Baje kolin "Gwanayen Afirka. Fasaha daga Cote d'Ivoire" (28.06. zuwa 05.10.2014) ya fito da aikinsu fili. A karon farko sun samu suna. Wannan zaunannen sigar mai gemu ya fito daga gwani Vérité.
Sunaye na wucin gadi
Ba dukkan sunayen masu sassaka ne aka gano ba. Saboda haka ne ga misali aka ba su sunayen yankunan da suka yi aiki a ciki. Gwani na Yasua (a duba hoto) ya rayu ne a yankin Guro da ke kusa da dajin kurmi. Wasu an ba su sunan "Gwanaye masu manyan hannu", "Gwanayen lemar tare rana" ko "Gwanayen kan zakara".
Daidaikun masu sassaka
An kwashe shekaru da yawa ana shirye-shiryen baje kolin, da zangonsa na farko ya kasance gidan tarihi na Rietberg da ke Zurich. Godiya ta tabbata ga nazarin sharen fage na masana fannin kayan tarihi, an samu masaniya game da gwanayen sassaka na ainihi. Domin an jima ana daukar cewa aikace-aikace ne na kabilu amma ba daidaikun masu sassaka ba.
Ba a san aikinsa ko amfaninsa ba
Ra'ayin masu nazarin kimiyya ya sha bambam game da asalin yankin "Gwanin lemar tare rana". Watakila ya rayun ne a yankin fadama da ke kudu kusa da babban birnin kasa Abidjan. Kayayyaki sassakarsa na da daukar hankali sosai: Suna rike da lema a hannu ko sanye da huluna a ka. Sun samo asali a farkon karni na 20 kuma watakila an yi amfani da su a matsayin kayan ado.
Dodon fuska na yaki
Sunan dan fasahar da ya sassaka wadannan dodannin fuska a 1940 Tame. Dan asalin yankin Dan ne da ke kan iyaka da Laberiya. Dodon fuska mai manyan idanu na ba wa mutane kwarjini da kwarin guiwa tare da tsorata abokan gaba. Tame ya fito daga iyali masu sassaka kuma ya koyi aiki daga wurin babansa. Fina-finan da ake nunawa lokacin baje kolin ya nuna yadda ake amfani da dodannin fuska wajen rawa
Bambamci da hadaka
Gumakan na nuna abubuwa mabambamta masu ban sha'a. Yayin da wasu 'yan fasaha suka sassaka gumaka masu kyawawan fuskoki da dogayen hanci da baki maras lebo, gunkin da Niokhité ya sassaka katta ne. Duk da bambamcin akwai wuraren da suka dace da juna. Wato ke nan yankunan ba su bambamta da juna ba.
Dan fasaha mai daraja
Ko wane dan fasaha ya gudanar da aikinsa ba bu katsalandan. Yanzu haka ana daraja aikinsu a wajen nahiyar Afirka. A makonnin baya an sayar da wata sassakar katako daga wani mai sassaka dan Cote d'Ivoire a kan kudi Euro miliyan 1,5. Kayayyakin sassaka da suka fi daraja su ne na Gwani I na Letaha (duba hoto) daga shekarar 1900.
Kayayyakin sassaka dabam-dabam
Bisa ga alamu gwani Yasua ya yi aiki ne tsakanin 1920 da 1940. Shi ya yi wa katakonsa bakin fenti. Ana iya gande aikinsa da mai budadden baki. Hular rufe fuska (duba Hoto) da babban baki da kunne mai fasalin cokali ya yi kama da aladen dawa da aka fi samu a Afirka. A jimilce masu nazarin kimiyya sun gano gumakan katako dabam-dabam 300.
Ci gaba da al'ada
Ana ci gaba da amfani da sanin masu sassakar. Jems Robert Koko Bi shi ne karamin mai sassaka a cikin mutanen hudu, wadanda aka baje kolin aikinsu a Bonn. Dan asalin yankin Baule ne. Yanzu haka dai yana zaune ne a birnin Essen, inda yake amfani da katako daga dajin Odenwald yana sassaka. "Kakan kanne" yake kiran wadannan kayayyakin sassaka, inda yake ci gaba da amfani da sanin kakannen kakannensa.
Kayayyakin sassaka masu daraja
Emile Guebehi da ya rasu a 2008 ya shahara wajen sassaka manyan gumaka masu sigogi mabambamta. A nan Guebehi ya gabatar da wani yanayi bayan mutuwar aure. Sassakar mai sigar mace da aka yi wa ado daga kugu zuwa cinya, ta samo asali ne daga zamanin da. Mazan na sanye da gajerun wanduna na zamani. Yanzu haka dai ana daraja kayayyakin sassakarsa a kasuwannin masu fasaha.