gwanatin jamus ta bukaci ganawa da yan bindiga da sukayi garkuwa da wata bajamusa | Labarai | DW | 01.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

gwanatin jamus ta bukaci ganawa da yan bindiga da sukayi garkuwa da wata bajamusa

Gwamnatin kasar Jamus tace tana bukatar tuntubar yan bindiga da suka yi garkuwa da wata bajamusa yar shekaru 43 da suke barazanar kasheta.

Ministan harkokin cikin gida na jamus Frank Walter Steinmeier,ya sanarwa manema labarai bayan taron komitin da aka kafa akan sace wannan mata a yau cewa gwmanati tana kokarin ganin kare lafiya da kuma ran matar da aka yi garkuwa da ita.

Sace wanna mata dai ya zama wani gwaji na farko da sabuwar shugabar gwamnati Angela Merkel wadda ta sha alwashin gyara dangardakar kasar jamus da Amurka da ta ja da baya akan batun mamayar Iraki take fuskanta.

Kodayake Steinmeier yace gwamnatin bata rigaya ta tuntubi yan bindigar ba haka zalika ana su bangare yan bindigar basu bada wani waadi ba ga ita gwamnatin Jamus.

Angela Merkel tace zata ci gaba da bin manufofin gwamnati da ta gada na taimaka horas da sojojin Iraki a wajen Irakin,amma ta yi watsi da batun aikawa da sojojin Jamus zuwa Iraki.