Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi Allah wadai da saɓa wa dokokin ƙasar da gwamnatin tarayya ke yi. | Labarai | DW | 26.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnonin jihohin Najeriya sun yi Allah wadai da saɓa wa dokokin ƙasar da gwamnatin tarayya ke yi.

Gwamnonin jihohin Najeriya sun ba da wata snarwa, inda suka yi kakkausar suka ga salon take dokokin ƙasar da keta hakkin ɗan Adam da gwamnatin tarayyar ƙasar ke yi. Ministocin dai sun ba da sanarwar ne yau bayan wani taron da suka yi a ran talatar da ta wuce, inda suka ce gwamnatin tarayyar na wuce gona da iri a matakan da take ɗauka a kwanakin bayan nan, musamman a jihohin Ekiti, da Anambra da kuma Plateau.

A ran alhamis da ta wuce ne dai shugaba Olusegun Obasanjo na tarayyar Najeriyan ya kafa dokar ta ɓaci, mai ci har wata 6, a jihar Ekiti inda ake ta fama da rikice-rikice, ya kori gwamnan da mataimakinsa, ya dakatad da majalisar jihar sa’annan ya naɗa wani kantoma wanda zai dinga tafiyad da harkokin jihar. Shugabanin dai ya bayyana cewa matakin da ya ɗaukan zai kare tafarkin dimukraɗiyya ne sa’annan kuma ya hana ɓarkewar halin ruɗami a jihar ta Ekiti.

Amma sanarwar da gwamnoni 36 na ƙasar suka bayar ta ce, wasu ƙusoshin gwamnatin na amfani da wasu matakai ne da ba su dace da kundin tsartin mulkin ƙasar ba, don cim ma burinsu na son zuci, abin da a zahiri take hakkin ɗan Adam ne. Irin waɗannan matakan dai, inji su, wato za su kasance wata barazana ce ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka da al’aumman ƙasar ke yi da juna.

A makon da ya gabata ne dai, kafin shugaba Obasanjo ya kafa dokar ta ɓacin, majlisar jihar Ekitin ta tsige gwamnan, Ayo Fayose, da mataimakinsa Biodun Olujinmi, saboda zargin cin hanci da rashawa da ake yi musu.