Gwamnatin Uganda ta tuhumi madugun adawa da cin amanar kasa | Labarai | DW | 15.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Uganda ta tuhumi madugun adawa da cin amanar kasa

Hukumomin kasar Uganda sun tuhumi babban madugun adawar kasar Kizza Besigye da laifin cin amanar kasa. Yan sanda na tuhumar Besigye da tunzura jamaá su yiwa gwamnatin shugaba Yoweri Museveni bore. Daruruwan magoya bayan madugun adawan sun gudanar da zanga zanga a manyan titunan kasar inda suka yi ta dauki ba dadi da yan sanda dake harba barkonon tsohuwa. Kizza Besigye shi ne babban wanda ke kalubalantar Museveni a takarar shugabancin kasar bisa tafarkin jamíyu da dama, wanda shi ne karo na farko a tarihin kasar cikin shekaru ashirin. Makwanni uku da suka gabata, Besigye ya koma kasar Ugandan bayan tsawon shekaru hudu yana gudun hijira a kasar Afrika ta Kudu. Ya taba zama likita mai kula da lafiyar shugaba Museveni kuma babban na hannun daman sa. Idan aka tabbatar da tuhumar da ake masa, yana iya fuskantar hukuncin kisa.