Gwamnatin Uganda da ´yan tawaye sun amince da shirin tsagaita wuta | Labarai | DW | 26.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Uganda da ´yan tawaye sun amince da shirin tsagaita wuta

A wani wani mataki na kawo karshen rigingimu a arewacin Uganda, gwamnati da ´yan tawayen kungiyar Lord´s Resisitance Army LRA sun sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da yaki. Yarjejeniyar wadda aka rattabawa hannu a birnin Juba na kasar Sudan, ya bukaci sassan 2 da su daina kaiwa juna hari da yada farfagandar nuna gaba daga ranar talata mai zuwa. Sassan biyu zasu ci-gaba da tattaunawa da nufin cimma yarjejeniya ta karshe wadda zata kawo karshen yakin wanda yayi sanadiyar mutuwar dubun dubatan mutane sannan kimanin miliyan biyu suka rasa matsugunansu a arewacin Uganda. Tun a ranar 4 ga watannan na agustan ´yan tawayen suka yi shailar tsagaita wuta, sannan ita kuma gwamnati a birnin Kampala ta yi wa shugabannin kungiyar ta LRA afuwa. To amma sun ki barin snsanonin su da ke kasar JDK kuma ba su halarci wajen taron yin sulhun ba don gudun ka da a kamasu a mika su ga kotun kasa da kasa dake tuhumarsu da aikata laifukan yaki.