1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Tunisiya za ta yi garambawul ga tattalin arziki

March 23, 2018

Gwamnatin Tunisiya ta tabbatar da matsayin gani gudanar da garambawul ga tattalin arziki da ke cikin mawuyacin hali.

https://p.dw.com/p/2usAO
Tunesischer Premierminister - Youssef Chahed hält Ansprache in Tunis
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Firaminista Youssef Chahed na kasar Tunisiya ya jaddada shirin gwamnatin kasar na sake fasalin kamfanonin gwamnatin cikin hanzari domin zaburar da tattalin arzikin kasar da ke yankin arewacin Afirka, wanda ke cikin mawuyacin hali gami da fama da gibin kasafin kudi.

Kungiyoyin kwadago sun nuna tirjiya bisa matakan da gwamnatin ke dauka saboda rasa guraben aiki da zabtare kudaden jin dadin mutane. An dade ana nuna adawa da matakin gwamnati na Tunisiya kan cefanar da kaddarorin gwamnati ga 'yan kasuwa, domin  garambawul ga tattalin arziki kasar.