1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bunkasa lantarki a Tanzaniya

January 16, 2017

Gwamnatin Tanzaniya karkashin Shugaba John Magufuli ta neman bashin Bankin Duniya domin bunkasa wutar lantarki a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/2Vscq
Tansania John Magufuli
Hoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Gwamnatin kasar Tanzaniya ta bukaci samun rancen kimanin dala milyan 200 daga Bankin Duniya don farfado da harkokin samar da wutar lantarki da ke cikin mawuyacin hali a kasar, kamar yadda ma'aikatar kula da makamashi ta tabbatar.

Shugaba John Magufuli, na bukatar ganin kasar ta Tanzaniya ta samu wadatacciyar wutar lantarki cikin farashi mai sauki domin bunkasa masana'antu, kuma yana ganin Bankin Duniya zai iya taimakawa matuka.