Gwamnatin Sudan ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya na Darfur | Labarai | DW | 30.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Sudan ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya na Darfur

Gwamnatin kasar Sudan ta amince da yarjejeniyar zaman lafiya na Darfur,wanda Kungiyar Tarayyar Afrika ta shawarta .

Wata sanarwa daga shugaban tawagar gwamnati wajen tattaunawar Abuja,Majzoub al-Khalifa,tace gwamnati tana mai tabbatar da amincewarta da wannan yarjejeniya,yace sun kuma yi imanin cewa,zasu iya magance duk wata matsala daka iya tasowa wajen kaddamar da yarjejeniyar,tsakanin dukkan bangarori.

Ya zuwa yanzu dai yan tawayen basu maida martani ba ga daftarin yarjejeniyar mai shafi 85,amma da yawa daga cikin shugabanninsu suna korafin cewa,yarjejeniyar bata cimma manyan bukatunsu ba,musamman ma game da madafun iko.

A yau ne waadin da AU ta dibarwa bangarorin da rikicin na Darfur ya shafa,na su kammala tattaunawar ta shekaru 2da nufin kawo karshen rikicin na Darfur.