Gwamnatin Sudan ta amince da tura sojojin MDD 100 a Darfur | Labarai | DW | 28.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Sudan ta amince da tura sojojin MDD 100 a Darfur

Gwamnatin Sudan ta amince da tura wasu dakaru kadan na MDD don taimakawa sojojin kungiyar tarayyar Afrika a lardin Darfur mai fama da rikici. Wata sanarwa da MDD ta bayar ta nunar da cewa a cikin watan janeru mai zuwa ake sa ran isar sojoji da ´yan sanda kimanin 100 a Darfur. A lokutan baya gwamnatin Sudan ta nuna adawa da girke dakarun MDD a Darfur. Wata sanarwa ta daban kuma ta ce gwamnati a Khartoum ta amince da girke wata rundunar hadin guiwa ta MDD da kungiyar AU, to amma har yanzu ba´a cimma matsaya akan wannan batu ba.