Gwamnatin Somalia ta zargi ƙungiyoyin islama da yunƙurin kame cibiyarta. | Labarai | DW | 18.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Somalia ta zargi ƙungiyoyin islama da yunƙurin kame cibiyarta.

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Somaliya, ta zargi ’yan ƙungiyoyin islaman ƙasar da yunƙurin kai wa cibiyarta hari, da yaɗa raɗe-raɗin cewa, dakarun Habasha sun kutsa cikin yankunan ƙasar, don dai su sami dalilin hujjanta aniyarsu. A jiya ne dai, mayaƙan ƙungiyoyin islaman, waɗanda tuni suka kame muhimman wurare a Somaliyan, suka kuma yi wa cibiyar gwamnatin riƙon ƙwaryar da ke garin Baidoa ƙawanya, suka ba da sanarwar cewa dakarun Habasha ɗari 3 sun kutsa cikin wasu yankuna na ƙasar.

Ana dai fargabar cewa ’yan islaman na da wata ajanda ne ta kame sabbin yankuna na ƙasar, da ƙaddamad da shari’a, yayin da suke ta ƙara samun angizo fiye da gwamnatin, wadda ba ta da wanni kwarjini balantana ƙarfin soji na kare harabobin ƙasar.

Tuni dai ƙasar Habasha ta musanta zargin da shugaban ƙungiyoyin islaman, Sheikh Sharif Ahmed ke yi mata. Gwamnatin Somaliyan kuma ta nanata cewa, zargin ba shi da wani tushe.