Gwamnatin Somalia ta yi fatan girke sojojin kiyaye zaman lafiya a kasar
January 1, 2007Talla
Bayan an fatattaki sojojin sa kai na kawance kungiyar kotunan Islama, yanzu gwamnatin wucin gadi ta Somalia na fatan girke dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afirka AU a kasar. FM Mohammed Ali Gedi ya fada a birnin Mogadishu cewa girke dakarun AU zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da daidaita al´amura a cikin kasar sa. Tare da taimakon sojojin Ethiopia a yau dakarun gwamnati suka karbi ikon kudancin kasar wanda ya kasance yanki na karshe a hannun mayakan na kotunan Islama. Bayan nasarar da suka samu, FM Gedi ya ce za´a ci-gaba da fatattakan ´yan Islama.