Gwamnatin Somalia ta umurci yan kasar da su mika makamansu | Labarai | DW | 01.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Somalia ta umurci yan kasar da su mika makamansu

Firaministan gwamnatin rikon kwarya ta Somalia Ali Muhammad Gedi ya umurci dukkan yan kasar ta Somalia da su mika makamansu cikin kwanaki uku masu zuwa.

Ya fadi hakan ne a wani taron manema labari daya kira a birnin Mogadishu.

Gwamnatin rikon kwaryar ta Somalia ta kuma yi tayin ahuwa ga mayakan islama da suka ajiye makamansu.

Tunda farko dai a yau rahotanni daga Somalia sunce mayakan islalan sun tsere daga yanki na karshe da suke rike da shi kusa da birnin Kismayo,sun kuma kama hanyarsu ta zuwa bakin iyaka kasar da Kenya,bayanda dakarun Habasha suke kutsawa zuwa Kismayo.

A ranar alhamis ne dakarun kotunan musuluncin suka fice daga birnin Mogadishu.