Gwamnatin Somalia ta saki jamiin majalisar dinkin duniya da ta tsare | Labarai | DW | 23.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Somalia ta saki jamiin majalisar dinkin duniya da ta tsare

Gwamnatin kasar Somalia ta sake jammin hukumar samarda abinci ta MDD bayan kusan mako guda yana tsare.Dakarun tsaro na Somalia da dama ne dai suka kutsa harabar ofishin MDD a birnin Mogadishu ranar laraba da ta gabata suka yi awon gaba da Idris Osman mai kula da rabar da abincin agaji a cikin birnin na Mogadishu.Jamian gwamnati sunce suna binciken Osman kann wasu laifuka da basu baiyana su ba.Tsare Osman ya janyo suka ga gwamnatin Somalia daga kasashe da dama.