1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Somalia ta nemi tallafi domin gudanar da bincike a game da harin ta´danci jiya

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buiy

Gwamnatin riƙon ƙwarya a Somalia, ta bukaci tallafi daga ƙasashen dunia, domin gudanar da bincike, bayan hare haren ta´adancin da ta su ka rutsa jiya, da shugaba Abdullahi Yusuf Ahmed, a birnin Baidoa.

Kakakin gwammnatin, Abdurahman Muhamad Nur, ya ce tunni, jami´an tsaro, sun fara binciko, alamun masu alhakin kai wannan hari,da ya hadasa mutuwar mutane 11 .

Ya ce alamomin farko,sun bayyana cewar akwai hannun kungiyar Alq´ida a cikin hari, ta la´akari da kammanin sa,da hare haren da ake kaiwa a Irak da Afghanistan.

Da dama daga jama´ar ƙasa, na zargin dakarun kotunan islama da ,kitsa harin, duk da sun bayana cewar babu hannun su ciki.

A halin yanzu dai, gwamnati ta ƙarfafa matakan tsaro a birnin Baidoa da kewaye, sannan gwamnati, ta jaddada kira na girke rundunar ƙasa da ƙasa a Somalia, saidai dakarun kotunan musulunci da ke riƙe da birnin Mogadiscio, na ci gaba da adawa da wannan mataki.