Gwamnatin Somalia ta bukaci Kenya da rufe bakin iyakokinta | Labarai | DW | 02.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Somalia ta bukaci Kenya da rufe bakin iyakokinta

Gwamnatin kasar Somalia ta roki kasar Kenya makwabciya da ta rufe bakin iyakokinta bayanda mayakan islama suka nufi bakin iyakar ta Kenya.

Firaminista Ali Muhammad Gedi ya kuma umurci dukkannin Somaliayawa dasu mika makamansu cikin kwanaki uku,yana mai mika tayin ahuwa ga mayakan islama da suka ajiye makamansu.

Gedi ya sabunta rokoonsa ga kungiyar taraiyar Afrika AU data aike da dakarun wanzar da zaman lafiya a kasarsa.

Komandan mayakan islama Yakub Moalim Ishak yace dakarunsu ba zasu dakatar da yakin ba.

Dakarun na islama,wadanda suke rike da kasar tun watan yuli,sun janye daga dukkan birane da suke rike dasu bayanda dakarun Habasha suka kaddamar kai farmaki kansu a ranar 20 ga watan disamba.