1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Somalia a karkashin jagorancin Abdullahi Yusuf ta koma gida daga Nairobi

zainab A MohammadJune 14, 2005

Fadar gwamnatin Somalia a garin Jowhar

https://p.dw.com/p/BvbN
Hoto: AP

A yaune jirgin dake dauke da shugaban kasar Somalia daya jima a birnin Nairobin Kenya ,tun bayan nadinsa ya doshi kasarsa domin cigaba da gudanar da harkokin mulki acikin gida.

Rahotannin sun tabbatar dacewa jirgin dake dauke da shugaba Abdullahi Yusuf na Somalia dai ya bar birnin Nairobin kasar Kenya,amma maimako ya doshi Somalia an karkatar dashi zuwa kasar Djibuti inda yan ne ya sauka.

Tun a jiya nedai kamfanin dillancin labaru na reuters da wasu kafofin yada labaru suka bayyanar dacewa,Shugaba Yusuf ya isa garin Jowhar dake Somalia domin nan ne zai kasance fadar gwamnati kamar yadda akasha mahawara akai a baya.

Babban sakatare na shugaban kasa Dahir Mire dai ya sanar da cewa a daren jiya ne jirginsa zai sauka a Jowhar.

Ya bayyana cewa jirgin shugaban kasar bai bar Kenya akan lokaci ba domin ya samu jinkiri,wanda har yakai ga tashi da yammaci.Mr Mire yace jirgin ya isa Jowhar cikin dare kuma karamin filin saukan jiragen sama na wannan gari bashi da wutan lantarki,wanda ya haddasa karkatar da jirgin dake dauke da shugaban kasan zuwa Djibuti.

Gwamnatin rikon kwarya na Somaliya dai na dauke da alhakin kawo karshen fada tsakanin shugabannin hauloli dake gaba da juna a wannan kasa.Tun da aka rantsar da ita a bara dai gwamnatin taciga da kasancewa a birnin Nairobin Kenya,dangane da rashin tabbas na inda fadar gwamnati zai kasance.

A jiya nedai shugaba Mwai Kibaki na Kenya ya gudanar da Liyafar ban kwana wa shugaban Somalia da mukarrabansa,kafin su tashi.

Kakakin shugaban na Somalia Yuszf Ismail Baribari ya fadawa manema labaru cewa,matukan jirgin ne suka zartar da sauya inda zasu sauka zuwa filin jirgi mafi kusa dake da naurori a kasar Djibuti dake makwabtaka da Somalia.

Yayi bayanin cewa shugaba Yusuf yayi muradin kwana koda guda ne a garin Jowhar.Jamiaai dai sun sanar dacewa shugaban Somaliyan zai dauki makonni biyu kama daga yau yana ziyaran kasashen dake yankin Gulf,inda ya farad a Qatar.

Ayayinda Kakakin nasa yace da zarar ya dawo zai yi rangadin aiki cikin kasar da kewaye kafin ya fara aikinsa nay au da kullun a matsayin shugaban kasa.

A ranar alhamis ne akesaran prime minsta Mohammed Ali Gedi zai bar Kenya zuwa Somalia.

Gwamnatin Somalia a karkashin jagorancin Shugaba Yusuf dai na mai zama na 14 inrinsa ,tunda Somalia ta fada rikice rikice ,bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Siad Barre a shekarata 1991.

Dubban mutane suka rasa rayukansu sakamakon wannan rikicin da yunwa daga balain fari,a wannan kasa mai yawan alumma million 10.