Gwamnatin riƙwan ƙwarya a Somalia ta ƙetara rijiya da baya | Labarai | DW | 30.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin riƙwan ƙwarya a Somalia ta ƙetara rijiya da baya

Gwamnatin riƙwan ƙwarya a ƙasar Somalia, ta ƙetara rijiya da baya, bayan ƙuri´ar da yan majalisar dokoki su ka kaɗa.

Yan majalisar, sun kaɗa wannan ƙuri´a domin kiffar da Praminista Mohamed Ali Guedi, da su ke zargi da zama karan farautar ƙasar Ethiopia, musamman bayan da ya bada goyan baya, ga hukumomin Addis Ababa, su jibge dakaru a ƙasar Somalia, domin yaƙar kotunan Islama wanda a halin yanzu ke riƙe, da babban birnin Mogadiscio.

A sakamakon ƙuri´a da aka kaɗa, yan majalisa 88 suka amince da kiffar da wannan gwamnati, daga jimmilar yan yan majalisa 215 da su ka halarci taron.

Jim kaɗan bayan wannan zaɓe, yan majalisar dokokin Somalia sun ba hamta iska, kamin jami´an tsaro su shiga tsakani.

A wannan mako,rikici ya ƙara rincaɓewa a ƙasar Somalia, bayan murabis ɗin ministoci 18, daga gwamnatin riƙwan ƙwarya, da kuma hallaka minista ɗaya, ranar juma´a da ta wuce.

A nata gefe ƙasar Masar, ta mussanta zargin da gwamnatin riƙwan ƙwaryar ta yi, na cewar fadar gwamnatin Alƙahira,ta bada taimakon makamai ga dakarun kotunan Islama.