Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Kirgistan ta soke zaɓen shugaban ƙasa | Labarai | DW | 19.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Kirgistan ta soke zaɓen shugaban ƙasa

Hukumomi a ƙasar Kirgistan sun bada sanarwa cewa an soke zaɓen shugaban ƙasar da aka shirya gudanarwa a cikin watan oktoba

default

Fadar majalisar dokoki ta ƙasar Kirgistan

 Gwamnatin riƙon kwarya a ƙasar Kirgistan ta soke zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a cikin watan oktba, tare da naɗa Mista Rosa Otounbaieva a masayin shugaban ƙasa har zuwa ƙarshen shekara ta 2011.

Nan gaba ne dai a cikin watan yuni za a tabbatar da naɗin ta hanyar yin ƙuria'ar jin ra'ayin jama'a da kuma tantance sabon kundin tsarin mulki na ƙasar.

Gwamnatin wucin gadin, wacce ta karɓi mulki a cikin watan aprilu, bayan wani bore da ya kada gwamnatin Kourmanbek Bakiev, ta sheda cewar a cikin watan oktoba zaɓen 'yan majalisar dokoki kaɗai za a gudanar

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       :  Ahmad Tijani Lawal