Gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙasar Kirgistan ta soke zaɓen shugaban ƙasa
May 19, 2010Talla
Gwamnatin riƙon kwarya a ƙasar Kirgistan ta soke zaɓen shugaban ƙasa da aka shirya gudanarwa a cikin watan oktba, tare da naɗa Mista Rosa Otounbaieva a masayin shugaban ƙasa har zuwa ƙarshen shekara ta 2011.
Nan gaba ne dai a cikin watan yuni za a tabbatar da naɗin ta hanyar yin ƙuria'ar jin ra'ayin jama'a da kuma tantance sabon kundin tsarin mulki na ƙasar.
Gwamnatin wucin gadin, wacce ta karɓi mulki a cikin watan aprilu, bayan wani bore da ya kada gwamnatin Kourmanbek Bakiev, ta sheda cewar a cikin watan oktoba zaɓen 'yan majalisar dokoki kaɗai za a gudanar
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Ahmad Tijani Lawal