1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nepal da ´yan tawaye sun fara tattaunawar yin sulhu

May 26, 2006
https://p.dw.com/p/Buwi
Gwamnatin Nepal da ´yan tawaye masu ra´ayin kwaminisanci sun fara shawarwarin wanzar da zaman lafiya da nufin kawo karshen rikicin da aka shafe shekaru da dama ana yi a wannan kasa. An fara taron ne a wani wurin wasan golf dake babban birnin kasar wato Kathmandu, sa´o´i kalilan bayan da sassan biyu suka amince su koma kan teburin shawarwari. Kafin a fara taron ministan cikin gida Krishna Sitaula ya fadawa manema labarai cewa babu wani bambamcin ra´ayi tsakanin gwamnati da ´yan tawaye a saboda haka taron zai yi nasara.