1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Nederlands ta yi murabus

June 30, 2006
https://p.dw.com/p/BusF
FM NL Jan Peter Balkenende ya mika takardun yin murabus din gwamnatinsa a hukumance ga sarauniya Beatrix. Wannan mataki zai share fagen gudanar da sabon zabe na gaba da wa´adi, wanda ake sa rai za´a yi a karshen wannan shekara. A jiya alhamis ´ya´yan jam´iyar D66 wadda ita ce karama a cikin gwamnatin kawance sun ajiye mukamansu a majalisar ministoci bayan yunkurin da aka yi na karbe takardun zama ´yar kasar NL daga ´yar asalin Somalia kuma ´yar majalisa Ayaan Hirsi Ali ya ci-tura. Ministar kula da zaman baki a cikin kasar ta NL Rita Verdonk ta fara tayar da batun karbewa Hirsi Ali takardun zama ´yar kasar bayan da ´yar asalin Somaliar ta amsa cewar ta ba da bayanai na karya a lokacin da ta gabatar da takardun neman mafakar siyasa. To amma daga baya an mayar mata da takardun zama ´yar kasar.