1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Najeriya tayi gargadin shiga kafar wando daya da masu neman tada hankali

default

Gwamnatin Najeriya tayi gargadin cewa,akwai wasu kungiyoyi da suke neman sake tada zaune tsaye a kasar,bayan tashe tashen hankula na watan daya gabata inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Ministan harkokin wajen Najeriya Frank Nweke,yace jamian tsaro sun shirya dakile ko cafke duk wasu shugabannin addini ko na siyasa da suke kokarin sake maimaita rikici da ya faru a watan daya gabata.

Nweke yace,wasu kungiyoyi da wasu mutane da suke adawa mulkin da shugaba Obasanjo,suna neman hanyoyi kota halin kaka, da zasu nunawa duniya cewa babu kwanciyar hankali a Najeriya.

A watan daya gabata dai mutane da damam sun rasa rayukansu a rikicin addini a Najeriya,tare kuma da ci gaba da yin garkuwa da maaikatan kanfanonin man fetur da akeyi a yankin Naija Delta.

Ministan na yada labarai yace,gwamnati ba zata sa ido taga wasu da suke neman mulki,sun kawo cikas ga kokarin kawo ci gaban kasar ta Najeriya ba.

A halin da ke ciki dai,jamaa na ci gaba da nuna damuwarsu game da rade radin cewa Obasanjo zai yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyara ta yadda zai samu damar tazarce.