1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta mika ragamar Arik ga Amcon

Gazali Abdou Tasawa
February 9, 2017

Gwamnatin Najeriya ta sanar a wanann Alhamis da karbar ragamar babban kamfanin sufurin jiragen sama na kasar mai zaman kansa na Arik Air domin hana masa dukushewa da ya kama hanyar yi. 

https://p.dw.com/p/2XHXF
Arik Air Airbus A330
Hoto: imago/R. Wölk

Jude Nwauzor Shugaban kamfanin Amcon da ke aikin ceto kadarori kasa a Najeriya wanda shi ne gwamnatin ta mika wa ragamar tafiyar da harakokin kamfanin na Arik Air ya ce gwamnatin ta dauki matakin ne domin kawo karshen abin da ya kira shirman da ake yi wajen tafiyar da wanann kamfani wanda a ya kai ga kasa biyan basussukan da ke kansa. 

A shekara ta 2006 ne dai aka kafa kamfanin sufurin jiragen saman na Arik Air wanda ya dinga aiwatar da kusan kashi 60% na jigilar fasinja a tsakanin biranen Najeriyar dama zuwa wasu manyan biranen kasashen waje kamar su London Johannesburg da New York. Kakakin kamfanin na Arik Air Ola Adebanji ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP da daukar wannan mataki ba tare da amma ya yi wani dogon jawabi a kai ba.