1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Najeriya ta aike da sojoji a jihar Abiya

September 30, 2010

Gwamnatin Tarayyar Najeriya na ƙoƙarin kuɓutar da yaran da ake garkuwa da su a kudu maso gabashin ƙasar.

https://p.dw.com/p/PRK3
'Yan bindiga a NajeriyaHoto: picture alliance / dpa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta aike da wasu sojoji kimanin 400 a jihar Abiya da ke yankin kudu maso gabashin ƙasar ,domin kuɓutar da wasu yara yan makaranta kimanin 15 da wasu yan bidiga ke tsare da su tun a farkon wannan mako. Masu aiko da rahotannin sun ce sojojin da ke cikin motocin sulke sun yi wa garin na Abiya zobe, sannan kuma al'amura sun tsaya cik bayan da aka rufe makarantu da shaguna da kuma bankuna.

Tun da farko dai 'yan bindigar sun buƙaci a biya su kuɗin fansa Naira miliyion 20. To amma daga bisani sun karya kuɗaɗen ya zuwa Naira dubu ɗari ukku da hamsin.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita : Halima Balaraba Abbas