1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Myanmar ta kare matakin gurfanar da 'Yar adawa a kotu.

May 22, 2009

Halinda ake ciki dangane da sake gurfanar da Aung San Suu Kyi

https://p.dw.com/p/HvGv
Aung San Suu KyiHoto: AP

Hukumomin ƙasar Nyamar ko kuma Bama sun kare kansu game da shari'ar da akewa shugabar 'yar'adawan nan ta kasar Aung San Suu kyi, tare da tabbatar da cewa za'a gudanar da shari'ar ta cikin adalci,duk kuwa da zargin saɓanin hakan da 'yan adawa da kuma ƙasashen waje keyi.

A wata sanarwa da ministan harkokin cikin gidan Bama, Nyan Win ya bayar tayi watsi da zargin da yan adawa keyi cewar,an shirya sake daure shugabar yan adawan ce, domin hana ta tsayawa zaben ƙasar da ake shirin gudanar wa a shekara 2010.

Hasali ma dai kasar ta Bama ta zargi yan adawan ne da alhakin anfani da ba'amirkan nan da yayi ninkaya ta wani tafki, zuwa cikin gidan Shugabar yar'adawar yan shekaru 63 dake ɗaurin talala, domin tilastawa ƙasashen waje matsawa hukumomin sojin ƙasar sako ta.

Aung San Suu Kyi Haus in dem sie unter Arrest steht in Myanmar.jpg
Gidan da ake tsare da itaHoto: picture-alliance/dpa

Wannan bayani da hukumomin ƙasar ta Bama suka bayar dai yazo ne a daidai lokacin da ƙasashen na duniya keci gaba da matsawa hukumomin sojin dasu sako, Suu Kyi data taba cin kyautar yabo na zaman lafiya na Nobel.Kuma kawo yanzu jakadun ƙasashen turai da dama ne ke sa ido a shari'ar, tare da lura da halin da take ciki a babban gida yarin kare kukan ka dake kasar. Jakadan ƙasar Rasha a Baman Mikhail Mgeladze na daya daga cikin jakadaun da suka halarci shariar da aka fara yiwa jagorar yar'adawar kuma yayi bayanin abinda ya ganewa idanun sa kamar haka..

yace"tana cikin koshin lafiya, tare da karsashi, kamar dai ba ta tare da wata damuwa. Koda yake dai akwai alamun damuwa tare da ita, amma ban da wannan, zamu iya cewar ana kulawa da ita,haka kuma ana tsare da ita ne a wani bene mai hawa biyu dake zama masaukin baki dake gidan kurkukun, abin da kuma bata koka da yanayin da take ciki ba"

Kawo yanzu dai aci gaba da shar'ar da ake Aung San Suu kyi, hukumomin sojin kasar sun gabatar da shedu 22 akasarin su yan sanda dake bada shedar cewar ba'amirken daya shiga gidan shugabar yan adawan mai suna John Yettaw ya gana da ita tare da daukan hotunan ta,duk da adawan hakan data nuna masa,tare kuma da kwashe kwanaki biyu cur a gidan.

Myanmar Birma Burma Aung San Suu Kyi und Ibrahim Gambari
Ibrahim Gambari da Suu KyiHoto: AP

Sai dai shugabanin yan adawan ƙasar na ciki da waje na cigaba da musanta wayannan zarge zarge na gwamnati, kamar yadda Nyo Ohn Myint kakakin jam'iyar yan adawan ta Nationale Lig for demokirat yayi bayani...

yace"ko shakka babu gwamnati na tsoron rawar da jagoran yan adawan zata taka ne a zaben shekara ta 2010 da za'a gudanar kwannan nan,kuma sun lura idan dai tana sake, zata basu mamaki, karka cire dayan biyu, wannan shine dalilin kama ta, kuma dalilin kitsa wacan sharri ke nan akan ta,wannan itace magana"

Wannan dai shine karo na biyu da wannan ba'amirke ke nunkaya zuwa gidan yar adawan,domin ko'a watan Nuwanban bara ya saci jiki zuwa gidan ta, amma taki ta gana dashi, tare da kai rahoton sa ga hukumomi, amma a wannan karon kamar yadda lauyan ta yayi bayani, Aung Suu Kyi bata mika shi ga hukumomi ba ne domin gudan kada a gallaza masa.

Muddin dai aka same su da laifi dukkanin su za su iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekeru biyar a gidan yari, lamarin da kuma zai maida hannun agogo baya a kokarin ganin an sako shugabar yar adawan ta Bama a karshen wannan wata.

Sai dai a yayin da wannan shari'a ke gudana, tuni ƙasar Amirka ta sabunta takunkuminta akan ƙasar, ita ma ƙungiyar Turai tayi alkawarin kara ɗaukan matakan takunkumi akan gwamnatin ta Nyamar ko Bama,tare da neman a hanzarta sako ta.

Mawallafi: babangida Jibril

Edita: Zainab Mohammed