Gwamnatin Lebanon ta kira taron gaggawa akan rahoton bincike na Mehlis | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Lebanon ta kira taron gaggawa akan rahoton bincike na Mehlis

Bayan bayyana rahoton MDD dangane da kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Libanon Rafik Hariri, gwamnatin Libanon ta kira wani taron gaggawa a yau asabar. Jami´an kasar sun ce taron zai samu halarcin shugaban Libanon Emile Lahud da kuma wakilan jam´iyar Hisbollah mai samun daurin gindin Syria. Rahoton da alkalin Jamus kuma mai bincike na musamman na MDD, Detlev Mehlis ya bayar ya nunar da cewa manyan jami´an Syria da na Libanon na da masaniya game da kisan gillar da aka yiwa Hariri. Har walayau rahoton binciken ya shafawa wasu ´yan´uwan shugaban Syria Bashar Al-Assad kashin kaji. A halin da ake ciki dan Hariri ya yi kira da a kafa wata kotun kasa da kasa wadda zata yi shari´ar mutanen da aka zarga da hannu a kisan mahaifinsa. Sannan Amirka da Birtaniya sun yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya dauki wani mataki akan Syria.