Gwamnatin Kabul ta kori manyan jami´an yamma biyu daga ƙasar | Siyasa | DW | 26.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Gwamnatin Kabul ta kori manyan jami´an yamma biyu daga ƙasar

Wannan mataki bai yiwa Majalisar Ɗinkin Duniya daɗi ba

default

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai

Kakakin shugaba Hamid Karsai, wato Humayun Hamidzada ya fito ƙarara ya tabbatar da cewa gwamnatin Afghanistan ta bayyana jami´an diplomasiyan biyu na ƙetare da cewa ba a buƙatarsu a cikin ƙasar, kuma ta yi kira garesu da su fice daga Afghanistan kafin ranar alhamis.

Mutanen biyu dai sun san Afghanistan ƙwarai da gaske kuma sun shafe shekaru da dama a cikin ƙasar, inda suke riƙe da manyan mukamai na jami´an diplomasiya. Michael Semple daga janhuriyar Ireland shi ne muƙaddashin wakilin ƙungyiar tarayyar Turai na musamman kuma jami´in ƙungiyar EU na biyu mafi girma a Afghanistan. Ya iya manyan harsunan ƙasar guda biyu wato Dari da Paschtu. Ɗaya kuma da aka kora shine Mavin Patterson ɗan Birtaniya daga yankin Ireland Ta Arewa. Shine masharwacin Majalisar Ɗinkin Duniya kan harkokin siyasa kuma yake matsayi na uku a mukami a tsakanin jami´an majalisar a kasar.

Gwamnatin Afghanistan na zargin Turawan biyu da zama barazana ga tsaron ƙasar ta Afghanistan. Ta ce mutanen biyu sun gana a asirce da ´yan tawayen Taliban a lardin Helmand mai fama da rikici dake kudancin Afghanistan. Aleem Siddique kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Kabul ya bayyana wannan hali da ake ciki da cewa rashin fahimta ne. Ya ce haƙiƙa manyan jami´an diplomasiyan biyu sun yi wannan ganawa a lardin na Helmand da shugabannin kabilun yanki amma ba wakilan Taliban ba. Siddique ya yi fatan cewa za a warware wannan rashin fahimtar cikin gaggawa. Ya ce yanzu haka ana tattaunawa da gwamnatin Afghanistan musamman da jami´an ma´aikatar harkokin waje. To amma ya jaddada cewa MƊD zata bi umarnin hukumomin Afghanistan yana mai cewa suna aiki tukuru don ganin jami´in su ya koma kasar nan ba dadewa ba don ci-gaba da tafiyar da aikinsa.

Siddique:

Ya ce “A halin da ake ciki babu wani abin da ke nuni da cewa ko za a yi musu shari´a ko kuma an zargin wani da aikata laifi. Hukumomin Afghanistan sun bayyana matsayinsu a fili cewa sun damu da abubuwan dake faruwa a lardin Helmand. Mun fahimci haka musamman bisa la´akari da matakan sojin da ba a dade da dauka ba kan yankin, har yanzu ana samun hauhawar tsamari.”

Rahotanni sun yi nuni da cewa tattaunawar da aka yi da shugabannin kabilun yankin ta mayar da hankali ne kan matakan da za a ɗauka don rage wahalhalu da mawuyacin halin da mazauna yankin ke ciki. Ɗaukacin jami´an diplomasiyan yamma na masu ra´ayin cewa ya kamata a ƙarfafa tattaunawa da shugabannin yankin don kawo karshen fadan da ake ci-gaba da yi a kudanci da kuma gabashin kasar ta Afghanistan. A bainar jama´a dai dai har yanzu gamaiyar ƙasa da kasa na adawa da yin ko wace irin tattaunawa da ´yan tawayen Taliban.