1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Jamus.

YAHAYA AHMEDNovember 11, 2005

Jam'iyyun SPD da na CDU-CSU sun cim ma yarjeneiyar kafa sabuwar gwamnatin tarayya.

https://p.dw.com/p/Bu4G
Shugabannin jam'iyyun gwamnatin.
Shugabannin jam'iyyun gwamnatin.Hoto: AP

Jami’an manyan jam’iyyun SPD da na CDU-CSU sun shafe kusan duk tsawon daren jiya suna ta tattaunawa cim ma yarjeneiyar kafa sabuwar gwamnatin hadin gwiwa ta tarayya, tsakaninsu. Da can ma, sai da aka yi ta zaton cewa, watakila su tsawaita shawarwarin har zuwa ran asabar. Amma ba zato ba tsammani, sai aka ba da sanarwar cewa, sun cim ma daidaito.

A halin yanzu dai jam’iyyun sun yarje kan wasu batutuwan da suka shafi matakan da sabuwar gwamnatin za ta dauka idan ta kama aiki. A cikinsu kuwa, har da na kara harajin nan na kayayyakin masarufi da cinikayya, wato VAT a turance a shekara ta 2007, daga kashi 16 cikin dari zuwa 19 cikin dari. Amma duk kudaden shigar da za a samu daga wannan karin, ba za a yi amfani da su wajen cike gibin kasafin kudin tarayya ba, inji Firamiyan jihar Saarland, Peter Müller:-

„Duk bangarorin sun yarje kan cewar, ba matakan tsimi kawai gwamnatin hadin gwiwar za ta dauka ba, za ta kuma gabatad da shirye-shiryen bunkasa harkokin tattalin arziki ta kuma tsaya daran dakau wajen ganin cewa an samad da guraban aikin yi ga matasa.“

Matsalar tattalin arzikin da ake huskanta a nan Jamus dai, ba wani abin sirri ba ne ga jam’iyyun. Haka kuma babban gibin kasafin kudin da ake da shi yanzu. Bisa cewar Firamiyan jihar Hessen, Roland Koch, a shekarar badi, gibin zai kai Euro biliyan 40. Duk da hakan dai, a shawarwarin, wasu jami’ai sun bayyana cewa, za a gabatad da wani shiri na farfado da tattalin arzikin kasar, shirin da za a kashe kusan Euro biliyan 25 a ko wace shekara har tsawon shekaru 4 a kansa. A kan wannan batun, Ludwig Stiegler, mataimakin shugaban jam’iyyar SPD, ya bayyana cewa:-

„Ba shiri ne na zuba jari ba, kamar yadda ake ta yada rade-radi a kansa. kari aka yi ga matakan da muka dauka tun lokacin yakin neman zabe. Matakan da suka shafi inganta harkokin ilimi, da tallafa wa kafofin tattalin arziki da dai sauransu.“

Har ya zuwa karshen tattaunawar dai, jam’iyyun sun yi ta samun sabani kan shawarar da SPD ta gabatar ta kago wata haraji ta musamman, wadda za a sanya wa masu hannu da shuni su dinga biya, ban da dai harajin albashi. Duk da cim ma yarjejeniyar da aka yi dai, akwai wasu batutuwan da jam’iyyun ba za su iya cim ma daidaito kansu ba, a lal misali a kan batun rufe duk tashoshin makaman nukiliya, ko kuma na yi wa tsarin fannin kiwon lafiya kwaskwarima.

A farkon mako mai zuwa ne dai jam’iyyun za su yi taronsu, inda `yan ko wace jam’iyya za su ka da kuri’un amincewa da yarjejeniyar. Hakan kuma shi ne zai share wa Angela Merkel fagen zamowa farkon mace, da ta taba jagorancin gwamnatin tarayya, a tarihin Jamus.