Gwamnatin Jamus ta fara kokarin ganin sako Jamusawa da akayi garkuwa dasu a Iraqi | Labarai | DW | 04.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Jamus ta fara kokarin ganin sako Jamusawa da akayi garkuwa dasu a Iraqi

Gwamnatin kasar Jamus ta baiyana damuwarta game da makomar wasu Jamasuwa 2 da akayi garkuwa da su a kasar Iraq.

Ministan harkokin waje Frank Walter Steinmeier ya fadawa taron manema labaru a birnin Berlin cewa jamian maaikatar harkokin wajen Jamus suna aiki ba dare ba rana wajen ganin an sako wadannan Jamusawa 2.

Ya kuma yi Allah wadai da sabon hoton bidiyoda aka nuna na wannan mata da danta.

Wadanda suka sace Hannalore Krause yar shekaru 61 da danta mai shekaru 20 muddin dai Jamus din bata janye dakarunta daga kasar Afghanistan cikin kwanaki 10 ba.

Watanni 2 da suka shige ne aka sace wadannan mutane a birnin Bagadaza.