Gwamnatin Jamus na bayan mista Steinmeier a batun na Kurnaz | Labarai | DW | 22.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Jamus na bayan mista Steinmeier a batun na Kurnaz

SGJ Angela Merkel da abokannen kawancen jam´iyar ta ta social democrat sun nuna goyon baan su ga ministan harkokin wajen F.-W. Steinmeier a game da rawar da ya taka lokacin tsare wani Bajamushe a sansanin Guantanamo. A cikin watan agusta da ya gabata jami´an Amirka suka saki Murat Kurnaz dan asalin Turkiya bayan ya shafe shekaru 4 a sansanin ba tare an yi masa shari´a ba. wani kakakin gwamnatin Jamus ya ce Merkel ta amince da Steinmeier kuma ta yi kira ga masu sukar lamirinsa da su jira sakamakon wani kwamitin bincike da majalisar dokoki ta kafa. Jam´iyun adawa na neman Steinmeier wanda a wancan jami´i ne a tsohuwa gwamnatin Gerhard Schröder da ya amsa cewa Jamus ta hana a saki Kurnaz tun a shekara ta 2002. A makon jiya Kurnaz ya fadawa kwamitin bincike cewa sojojin Amirka sun ci zarafin sa lokacin da yake tsare.