1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Jamhuriyar Chek ta rushe

Suleiman Babayo
January 17, 2018

Gwamnatin Jamhuriyar Chek ta Firaminista Andrej Babis ta yi murabus sakamakon kuri'ar yanke kauna da majalisar dokoki ta kada.

https://p.dw.com/p/2r2OK
Tschechien Andrej Babis, Premierminister
Hoto: Reuters/D.W. Cerny


Firaminista Andrej Babis na Jamhuriyar Chek da ministocinsa sun yi murabus kwana guda bayan kada kuri'ar yanke kauna da majalisar dokokin kasar ta kada. Sai dai Shugaba Milos Zeman ya ce yana shirye ya sake bai wa firaminista mai garin gado Babis wata dama idan zai iya sake samun rinjaye a masalisar dokoki bayan ya tattauna da jam'iyyu. Amma tuni Andrej Babis hamshakin mai arziki ya kawar da yuwuwar shiga sabuwar gwamnatin da za a kafa duk da cewa jam'iyyar da yake jagoranci take da rinjaye a majalisar dokokin.

Karkashin dokokin kasar ta Jamhuryar Chek shugaban kasa yana da izinin bayar da dama sau biyu ga jam'iyyu domin kafa gwamnati idan aka rasa, mai shugaban majalisar dokoki yake da dama ta uku kuma ta karshe, kuma yanzu haka dan jam'iyyar firaminista mai barin gado yake jagorancin majalisar dokokin.