gwamnatin Ivory Coast ta amince da shugaban yan tawaye a matsayin Firaminista | Labarai | DW | 27.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

gwamnatin Ivory Coast ta amince da shugaban yan tawaye a matsayin Firaminista

Gwamnatin kasar Ivory Coast ta amince da nadin shugaban yan tawaye Guillaume Soro a matsayin firaminista karkashun wani shiri na sake hadin kann kasar.

Shugaba Laurent Gbagbo yace mai yuwane a kafa sabuwar gwamnatin nan da karshen mako.

Shide Soro shine ya jagoranci yunkurin juyin mulki kann Gbagbo a 2002,wanda ya haddasa yakin basasa da ya rabe kasar kashi biyu tsakanin gwamnati da kuma yan tawayen.

Makonni uku da suka shige ne dai bangarorin biyu suka rattaba hannu kann yarjejeniyar zaman lafiya wadda ta share fagen kafa sabuwar gwamnati.

Tuni dai kuma yarjejeniyar ta samarda kafa cibiyar rundunar soji ta hadin gwaiwa wadda zata maida hankali kann rushe mayakan sa kai daga bangarorin biyu.