Gwamnatin Iraqi ta ce za ta saki fursunoni dubu 2 da ɗari 5 da ke tsare a gidajen yarin ƙasar. | Labarai | DW | 07.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Iraqi ta ce za ta saki fursunoni dubu 2 da ɗari 5 da ke tsare a gidajen yarin ƙasar.

Firamiyan Iraqi, Nouri al-Maliki, ya ba da sanarwar cewa nan ba da daɗewa ba, gwamnatinsa za ta saki fursunoni dubu 2 da ɗari 5 da jami’an tsaro ke tsare da su a gidajen yarin ƙasar, a cikin wani mataki na cim ma tuntuɓar juna da haɗin kan al’umman Iraqin. An dai kafa wani kwamiti, inji Firamiyan, wanda zai yi nazari kan fursunonin da suka cancanci a sako su, amma masu nuna biyayya ga tsohon shugaba Saddam Hussein da jam’iyyarsa ta Ba’ath, bas a cikin waɗanda za a yi wa afuwar.

A yau laraban nan ne dai ake sa ran sako farkon rukunin mutanen da aka tsaren, wanda ya ƙunshi fursunoni ɗari 5.

A halin da ake ciki a Iraqin dai, mun sami rahotannin cewa, wani bam ya ta shi cikin mota a unguwar Amal na birnin Bagadaza, inda mutane 5 suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 15 kuma suka ji rauni. Hukumar ’yan sandan ƙasar ta ba da sanarwar cewa, jami’an tsaro sun gano kawunan mutane 9 da aka daddatse a garin Baquba da ke arewacin birnin Bagadazan. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka gano hakan a wannan yankin, a cikin ’yan kwanakin da suka wuce.