Gwamnatin Iraki zata kara ba da kariya ga lauyoyi a shari´ar da ake yiwa Saddam Hussein | Labarai | DW | 22.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Iraki zata kara ba da kariya ga lauyoyi a shari´ar da ake yiwa Saddam Hussein

Gwamnatin rikon kwaryar Iraqi ta ba da sanarwar daukan tsauraran matakan tsaro don ba da kariya ga lauyoyi a shari´ar da ake yiwa Saddam Hussein. Hakan dai ya zo ne bayan wasu ´yan bindiga da suka bad da kama a cikin kayan sarki suka sace daya daga cikin lauyoyin kuma suka yi masa kisan gilla a birnin Bagadaza. A jiya juma´a aka gano gawar lauyan wanda dan sunni ne wato Saadoun Sugaiyyer Al-Janabi a kusa da wani masallaci a babban birnin na Bagadaza, sa´o´i kalilan bayan da ´yan bindigar suka sace shi daga ofishin sa. Yanzu haka dai sauran lauyoyi dake kare jami´an tsohuwar gwamnatin Iraqi da ake yiwa shari´a sun bukaci da a kara ba su kariya.