Gwamnatin Iraki tana neman kawo karshen IS | Labarai | DW | 19.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Iraki tana neman kawo karshen IS

Gwamnatin Iraki ta kaddamar da farmakin kwace yammacin birnin Mosul daga hannun mayakan IS, lamarin da ke zama matakin karshe na tarwatsa tsagerun.

Firaminista Haider al-Abadi na Iraki ya bayyana cewa sojoji sun kaddamar da farmaki domin kwace yammacin birnin Mosul daga hannun tsagerun kungiyar IS. Hakan ya zo watanni hudu bayan sojojin sun farma birnin da ke zama tungar karshe na tsagerun na IS.

Kwace yammacin birnin Mosul zai zama wani aiki mai wahala saboda yadda masu ikirarin jihadi suka mamaye yankin, inda tuni aka kara yawan jami'an tsaro domin tabbatar da samun nasarar dakarun Iraki a wannan gagarumin aiki.