1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Iraki ta girke dubun dubatan dakaru a birnin Bagadaza

June 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buu0

An dauki tsaurara matakan tsaro mafi girma a birnin Bagadaza tun bayan da dakarun Amirka suka mamaya kasar Iraqi. Kimanin sojojin hadin guiwa na Iraqi da na rundunar kasashen waje dubu 40 ne yanzu haka aka girke a wurare daban-daban na babban birnin na Iraqi, don dakile tashe tashen hankula tare da farautar masu ta da kayar baya. Wata sanarwa da FM Nuri al-Maliki ya bayar ta nunar da cewa an haramta daukar makamai kana an kafa dokar hana fitar dare tare da hana zirga-zirgar motoci a lokacin sallar juma´a. A kuma halin da ake ciki ´yan sandan Jamus a filin saukar jiragen sama na birnin Frankfurt sun cafke wani dan Iraqi da ake zargi da taimakawa sojin sa kai na kungiyar Ansar al-Islama da makudan kudade. Ana zargin kungiyar da alaka da kungiyar al-Qaida a Iraqi. Mutumin mai shekaru 36 shi ne na 7 da ake tuhuma da alaka da wannan kungiya a nan Jamus.