Gwamnatin Hukumar Falasɗinawa ta yi murabus. | Labarai | DW | 14.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Hukumar Falasɗinawa ta yi murabus.

Duk mambobin majalisar ministocin Hukumar Falasɗinu, wadda ƙungiyar Hamas ke yi wa jagoranci, sun miƙa takardun murabus ɗinsu ga Firamiyan Falasɗinawan Isma’il Haniya, gabannin kafa wata sabuwar gwamnatin haɗin kai tsakanin ƙungiyar Hamas ɗin da ƙungiyar Fatah ta shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas. Wani kakakin gwamnatin Falasɗinawan ne ya tabbatar wa maneman labarai hakan a birnin Ramallah.

Rahotanni dai sun ce shugaban Falasɗinawan Mahmoud Abbas ya amince da kafa gwamnatin haɗin kan da ƙungiyar Hamas ne a wani yunƙurin cim ma ɗage takukunkumin da ƙasashen Yamma suka sanya wa Hukumar Falasɗinawan tun da

’yan ƙungiyar Hamas suka lashe zaɓen da aka gudanar a farkon wannan shekarar.