Gwamnatin hadaka a palasdinu | Labarai | DW | 09.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin hadaka a palasdinu

A yau ne yan Hamas da suka samu nasarar Zabe a Yankin Palasdinu da jammiyar Fata datasha kaye suka koma tattaunawa a dangane da kafa gwamnatin hadaka a wannan yankin,bayan dage zaman da yini gudu kamar yadda aka tsara da farko.

Wannan tattaunawa tsakanin shugaban yan majakisa na bangaren Fata Azzam al-Ahmed da takwaransa na bangaren Hamas Mahmud al-Zahar,na gudana ne a gidan Zahar dake zirin Gaza.

Wannan tattaunawa wanda ke zaman na karo na biyun irinsa a makonni biyu da suka gabata ,ya biyo bayan musayar yawu ne tsakanin yan majalisar a wannan makon.Yan majalisar Fata dai sun fice,daga zaman majalisar ne bisa zargin Aziz Dweik,na Hamas da kawo koma baya cikin yunkurin cimma wata yarjejeniya.

Idan dai zaa iya Tunawa Prime minista Ismail Haniya mai jiran gado,yace duk dacewa kasashen yammaci sun sanya Hamas cikin sawun kungiyoyin taada,zai gayyaci sauran jammiyun siyasar yankin palasdidu da suka hadar da Fatah ,domin kafa sabuwar gwamnatin hadin kann kasa.

 • Kwanan wata 09.03.2006
 • Mawallafi Zainab A mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7Y
 • Kwanan wata 09.03.2006
 • Mawallafi Zainab A mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu7Y