Gwamnatin Faransa ta farfado da tsohuwar dokar ta baci a kasar | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Faransa ta farfado da tsohuwar dokar ta baci a kasar

Bayan an shafe dare na 12 a jere ana tashe tashen hankula a birane da garuruwa na kasar Faransa, gwamnati ta farfado da dokar ta-baci da aka kafa ta shekaru 50 da suka wuce. Bayan wani taron majalisar zartaswa, ministan harkokin cikin gida Nicholas Sarkozy ya sanar da cewa ana iya kafa dokar hana yawo a dukkan yankunan da ke fama da tarzomar matasa marasa galihu. Da farko FM Dominique de Villepin ya sake jaddada cewar gwamnati zata dauki dukkan matakan da suka wajaba don maido da bin doka da oda a fadin kasar baki daya. To sai dai gwamnati zata jira kafin ta girke sojoji a unguwannin da ake fama da matsalolin. A cikin daren jiya ma matasa sun ci-gaba da tarzoma inda suka yi ta bankawa motoci da gine-gine wuta.