1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Falasdinawa ta yi maraba da agajin da za´a tura mata

May 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buyu

Gwamnatin Falasdinawa karkashin jagorancin kungiyar masu matsanancin ra´ayi ta Hamas, ta yi maraba da shawarar da sassan nan 4 dake shiga tsakani a rikicin yankin GTT suka yanke ta bawa Falasdinawa taimakon kudi. Kakakin majalisar ministoci Ghazi Hamad ya fada a birnin Gaza cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage wahalhalun da al´umar Falasdinawa ke fuskanta. Amma a lokaci daya Hamad ya nuna bacin ransa game da sharadin da aka gindaya kafin ba da wannan taimako. A wani labarin kuma FM Isra´ila Ehud Olmert ya ce nan da kasa da watanni 6 masu zuwa Isra´ila zata fara shata kan iyakokinta na radin kanta idan kungiyar Hamas ta ki amincewa da ´yancin wanzuwar kasar Bani Yahudu.