Gwamnatin Ehud Olmert na Israela ta fara digirgire | Labarai | DW | 28.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Ehud Olmert na Israela ta fara digirgire

Faraministan Israela, Ehud Olmert ya fara tunanin makomar sa a siyayance, bayan da yan jam´iyyar Labo suka fara kada kuri´ar zaben sabbin shugabanni.Ana dai tunanin cewa wannan zabe ka iya yin tasiri, a game da gwamnatin hadin gwiwar da Mr Olmert kewa jagoranci.Daga cikin masu fafata neman shugabancin na jam´iyyar ta Labo, akwai tsohon faraministan kasar, Mr Ehud Barak da kuma sabon jini wato Ami Ayalon.Tuni dai yan takarar biyu suka yi alkawarin aiki tare, don kawo karshen shugabancin na Mr Olmert.Da yawa dai daga cikin yan siyasar kasar na zargin gwamnatin ta Olmert, da rashin nuna adalci a lokacin yakin da kasar ta gwabza da Libanon.