Gwamnatin Chadi ta sake zargin Sudan da kai hari a cikin kasarta. | Labarai | DW | 28.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Chadi ta sake zargin Sudan da kai hari a cikin kasarta.

Kasar Chadi ta zargi sojojin sama na makwabciyarta Sudan da kai harin bama-bamai akan garuruwa guda hudu dake kan iyakar ta da lardin Darfur mai fama da rikici a yammacin Sudan. Gwamnatin shugaba Idris Deby ta ce a jiya Sudan ta kai farmaki akan garuruwan Bahai da Tine da Karyari da Bamina, inda ta lalata gidaje. To amma ba ta ba da labarin salwantar rai ko jikata ba. gwamnati a birnin N´djamena ta yi kira ga kungiyar tarayyar Afirka AU da da MDD da su yi Allah wadai da hare haren da aka kai kan ´yan Chadi masu son zaman lafiya. A farkon wannan makon Chadi ta zargi Sudan da marawa ´yan dake kutse cikin yankunanta baya.