Gwamnatin Burma ta dauki sabon salo | Labarai | DW | 02.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Burma ta dauki sabon salo

Gwamnatin mulkin sojin kasar Burma ta katse layin yanar giza gizan sadarwa na Internet dake fadin kasar. Daga dai tun safiyar jiya alhamis ne, gwamnatin kasar ta saka dokar ta baci a layukan sadarwa na Internet din.Bugu da kari gwamnatin ta kuma ce ba zata kara wa´adin aikin wakilin Mdd a kasar ba, wato Charles Petrie.Kafafen yada labarai dai sun rawaito wani jami´in Mdd a birnin Rangoon, na tabbatar da wannan labari.Matakin na Burma dai yazo ne kwana daya kafin zuwan wakilin Mdd na musanman, wato Farfesa Ibrahim Gambari. Hankalin duniya dai ya karkata kann kasar ta Burma ne, bayan da sojin kasar suka bude wuta kann mai uwa da wabi ne kann masu zanga zangar adawa da gwamnati. Masu zanga zangar dai na bukatar kasar, dawowa izuwa tafarki ne na mulkin dimokradiyya.