1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Belgium ta shigar da Limaman Islama cikin jerin Limaman addinai da take tallafa musu

December 19, 2007

Wannan shirin wani gagarumin canji ne akan turbar da ta dace

https://p.dw.com/p/Cdf3
Musulmi na salla a wani masallaci a BrusselsHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Mu Kewaya Turai, shirin ke kawo muku batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, al´adu, zamantakewa da kuma dangantaka tsakanin ƙasashen nahiyar Turai.

A ƙasar Belgium hukuma ce ke ɗaukar nauyin horas da malaman addini da suka kama daga na ɗarikar Katholika, Evangelika da fada-fada na ɗarikun Orthodox da na malaman addinin Yahudawa. Babu wata ƙasa a nan nahiyar Turai da ta ke yin haka. Kawo yanzu limaman addinin islama ne kaɗai ba sa cin gajiyar wannan shiri na biyan kuɗin horas da su. To amma yanzu abubuwa zasu canza. A halin da ake ciki yanzun haka a karon farko yankin da ke magana da harshen Faransanci a ƙasar ta Belgium ya amince da wasu masallatai inda daga watannan na desamba ya fara ba da kuɗin horas da limamai guda 50 a wannan yanki. Wannan shirin bai tsaya a nan ba, domin nan gaba hukumomin yankin zasu ƙara yawan limaman da suke ɗaukar nauyin karatunsu da albashinsu. Ga gamaiyar musulmin wannan yanki kuwa hakan wani babban sauyi ne akan turbar da ta dace. Wakiliyar Deutsche Welle Barbara Mohr ta kai ziyara a ɗaya daga cikin masallatan dake a garin Tournai dake kusa da kan iyaka Belgium da Faransa, da hukuma zata ba da taimakon kuɗin horas da limaman su. Muna ɗauke da karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni Mohammad Nasiru Awal zan gabatar.

Imam:

Kiran sallar Juma´a ke nan a masallacin Abu-Bakr dake a karamin garin Tournai dake bakin iyakar ƙasar belgium da Faransa. Limamin masallacin shi ne Lamrani Lakrari kuma a kullum shi ke limanci a wannan masallaci.

Wasu al´umar musulmi dake salla a wannan masallaci na masu ra´ayin cewa hukuma ta na son ta wuce gona da iri wajen horas da limamai. Daga cikin su kuwa akwai Hassan Houddain wanda ya ce ko da yake suna maraba da wannan shiri amma suna saka ayar tambaya ga manufar hukuma.

Houddain:

“Wannan dai wani ƙaramin masallacin ne dake cikin wannan ƙaramar gamaiya. Mu da kanmu ba zamu iya ɗaukar nauyin limami ba balantana mu ba shi albashi. Saboda haka abin da muke yi kawo yanzu shi ne muna neman taimako daga wasu masallatan da su aiko mana da limamai daga lokaci zuwa lokaci. A wani lokaci waɗanda ke da ilimin addini daga cikin wannan gamaiya suke yi mana limanci da sauran ayyuka na limamai. To amma ba zasu iya maye gurbin wani limami ko malami dake da ilimi ko karatun addini ba.”

Tun wasu makonni da suka gabata Lamrani Lakrari ke kula da ayyukan gamaiyar a garin Tournai. Bayan ya kammala karatun jami´a a fannin aikin lauya da addinin Islama Lakrari ya yi limanci na tsawon shekaru 20 a Faransa. Yanzu dai ya koma garin Tournai inda ya ce zai ci-gaba da zama domin gwamnatin Belgium ta dauki nauyin biyan albashinsa.

Huddain:

“Wannan wani gagarumin canji ne a garemu. A ƙarshe mun samu limamin kanmu. Saboda haka daga yanzu mun daina tunanin yin hayar wani limami daga wani masallaci.”

Malaman addini dake karkashin kulawar gwamnati ba baƙon abu ba ne a Belgium. Tun shekaru da dama da suka wuce ƙananan hukumomin ke daukar nauyin ayyukan fada-fada na kirista da kuma limaman yahudawa, amma bisa sharaɗin cewa an bukaci haka daga wurin hukuma kana kuma ba a karya wata doka ba. Wannan dai wani abu da ba ya da kishiya a Turai. Yanzu dai wani masallaci na farko ya samu nasarar shiga jerin amintattun wuraren ibada da hukumomin ƙasar ta Belgium ke ɗaukar nauyin su. Hakan kuwa wata kyakyawar alama ce ga masu salla a wannan masallaci dake Tournai kamar yadda wannan matar ta nunar.

Muslima:

“Ko wace gamaiya ta cancanci a rika tallafa mata. Yanzu da yake hukuma ta ɗauki nauyin yin haka to ke nan akalla limamin mu ba zai ji kamar ya na rayuwa ne akan sadaka ba. Domin aikin sa bai da dangantaka da sadaka. Aiki ne na ibada da yiwa jama´a hidima saboda haka ya kamata a saka masa.”

Kawo yanzu biyan limamai a Belgium ya banbanta kwarai daga masallaci zuwa masallaci wato ya na danganta ne da yawan sadakar da masallaci ya tara. To amma yanzu hukuma zata ba su albashi daidai wa daida, inji Imam Lakrari sannan sai ya ƙara da cewa.

Lakrari.

“Wani abin ban sha´awa a nan shi ne za a ba wa dukkan limaman matsayi ɗaya ba da an nuna banbanci ba ko a Brussels ko a Tournai ko Mense ka ke aiki ba. Yanzu dukkan mu mun zama jami´an ma´aikatar ilimi da yada al´adu.”

Ba tsarin albashin ne kadai ke zaman sabon abu ga limaman ba, a´a zai kuma ba su wani ´yanci daga gamaiyarsu. An dai sha yin ƙorafin cewa limaman da masallatai ke biyan su albashi da wuya suke iya fitowa fili su fadi ra´ayinsu.

Lakrari:

“A cikin shekaru 20 da na shafe ina limanci ban taɓa jin shakkan faɗin gaskiya ko bayyana ra´ayi na ba. To amma wasu limaman musamman waɗanda ke rayuwa akan sadaka, sun gwammace da su kama bakinsu su yi shiru maimakon su faɗi ra´ayin su. Yanzu kam an magance wannan matsala bayan da hukuma ta amince da mu.”

A cikin wata huɗuba da ya yi kwanakin nan Imam Lakrani ya ce mutum kirki shi ne wanda ke neman zaman lafiya da kowa ba tare da nuna banbanci na addini ba. Bisa ga dukkan alamu wannan saƙo ya samu karɓuwa a tsakanin gwamnatin ƙasar ta Belgium, wadda ta cika alƙawarin da ta ɗauka na daidaita matsayin albashin limaman musulmi, kiristoci da kuma na Yahudawa.