Gwamnatin Amurika ta maida ga rahoton Majalisar Dinki Dunia a game da Gwantanamo | Labarai | DW | 17.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin Amurika ta maida ga rahoton Majalisar Dinki Dunia a game da Gwantanamo

Gwamnatin Amurika ta soki lamirin Majalisar Dinkin Dunia , bayan da komitin Majalisar mai kulla da kare hakokin bani adama, ya hiddo rahoto jiya alhamis,a game da gidan wakkafin Gwantanamo na kasar Cuba.

Wannan rahoto ya bayyana ukuba da azaba da Amurika ke ganawa, wanda ke tsare a Gwantanamo, a dangane da haka ya bukaci a rufe wannan gidan yari, a kuma gudanar da shariá ga pirsinonin, kokuma a sallame su.

Gwamnatin Amurika ta ce rahoton na Majalisar Dinkin Dunia babu kanshi gaskiya a cikin sa, kuma batun rufe wannan gidan kuruku, ba abu ne mai yiwuwa ba, inji kakakin gwamnatin Amurika, wanda ya kara da cewa, rahoto ne kawai, na son zuciya da aka bugga, don bata sunan Amurika.