1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Amirka ta jaddada ƙudirin cigaba da aiki da Afghanistan

May 11, 2010

Bayan da mahukuntan Amirka suka zargi gwamnatin Karzai da cinhanci da rashawa yanzu shugabanin biyu sun ƙudirin kyautata dangantakar ƙasashensu

https://p.dw.com/p/NKuk
Shugaba Barack Obama tare da Shugaban Afghanistan Hamid KarzaiHoto: AP

Gwamnatin Amirka ta jaddada ƙudirin cigaba da aiki na ƙud da ƙud tsakanin ta da gwamnatin Afghanistan.

Jakadan shugaban Amirka a ƙasashen Afghnaista da Pakistan Richarg Holbrooke ya jaddada hakan a lokacin da yake ƙarbar shugaba Hamid Karzai dake ziyarar aiki a Amirka.

A 'yankwanakin nan dai ankai ruwa rana tsakanin Amirkan da Afgahanistan bayan da hukumomin Amirka suka zargi gwamnatin shugaba Hamid karzai da kasa taɓuka komai wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Inda shi kuma Karzai ya zargi ƙasar Amirka da shirya maguɗin zaɓen ƙasa daya gabata.

Ko'a watan Maris saida shugaba Barack Obama ya kai ziyarar bazata zuwa birnin Kabul inda ya jaddada goyoyn bayan Amirkan wajen yaƙi da 'yan ƙungiyar Taliban.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Abdullahi Tanko Bala