1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Amirka na ɗari-ɗari ga shawarar tuntuɓar Siriya da Iran don kwantad da ƙurar rikici a Iraqi.

November 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buc6

Shugaban Amirka, George W. Bush, na nuna rashin gamsuwa ga shawarar neman taimako daga Siriya da Iran wajen samo bakin zaren warware rikici da tashe-tashen hankulla a Iraqi. Ya kuma gargaɗi ’yan jam’iyyar Democrats, waɗanda suka lashe zaɓen majalisun ƙasar da aka gudanar a makon da ya gabata, da kada su bari zumuɗin sakamakon zaɓen ya sanya su ɗaukan matakan gaggawa na janye ko kuma rage yawan dakarun Amirka a Iraqin. Bush ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar bayan shingen da ya yi jiya, da mambobin wani kwamitin da aka naɗa don ya yi nazari kan hanyoyin warware rikicin Iraqi. A yammacin jiyan ne kuma, shugaban ya yi shawarwari da Firamiyan Isra’ila, Ehud Olmert, wanda ya kai masa ziyara a fadar White House. Bayan ganawar dai, Olmert, ya bayyana goyon bayansa ga shirin da Amirka ke jagoranta, na ganin an sanya wa Iran takunkumi. Amma ya kuma ce Isra’ila, ba ta da sha’awar yin taho mu gama da Iran ɗin.